24 Mayu 2021 - 16:25
An Sake Haramta Macin Goyan Bayan Falasdinu A Faransa

A mako na biyu a jere, hukumomin Faransa sun haramta yin macin goyan bayan Falasdinu a birnin Paris.

ABNA24 : Kungiyoyin kwadago, jam'iyyun siyasa da kungiyoyin kare hakkin dan adam da dama ne suka shirya zanga zangar ta goyan al’ummar Falasdinu, da kuma yin tir da laifukan yaki da Isra'ila ke aikatawa kan al’ummar Falasdinu.

Masu zanga-zangar na zargin hadin kan Shugaban Faransa Macron da laifukan yakin da Isra’ilar ke aikatawa.

A makon da ya gabata dai masu zanga zangar sun bijirewa haramcin macin inda suka fito nuna goyan baya ga Falasdinu, lamarin da ya rikide zuwa dauki ba dadi, tsakanin masu zanga zangar da ‘yan sanda a wasu sassan birnin na Paris.

342/